On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An Sake Zabar Hajiya Hadiza Balarabe A Matsayin Yar Takarar Mataimakin Gwamna A Kaduna.

Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna.

Dan Takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC, Sanata UbaSani, ya bayyana mataimakiyar gwamnan jihar, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, a matsayin wadda zata yi masa takarar mataimaki a zaben gwamna na shekara mai zuwa.

Hajiya Hadiza Balarabe, Wadda  ta kasance mataimakiyar  Gwamna Nasir El-Rufai  tun daga  shekarar 2019 bayan mataimakinsa na lokacin, Architect Barnabas Bala Bantex, ya ayyana neman kujerar Sanata, Koda yake da  farko a cikin watan maris taki karbar  tayin da gwamna El-rufa’I  yayi mata kafin kuma daga bisani ta amince.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a  daren ranar Litinin, Sanata  Uba Sani ya ce bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, Yana  farin  cikin  sanar da cewa ya zabi Hadiza Balarabe a matsayin wadda  zata yi masa takarar mataimaki.