On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

An Sako karin Wasu Yahudawa 11 Da Kuma Falasdinawa 33, A yayin Da Aka Tsawaita Wa’adin Tsagaita Bude Wuta

Kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta sake sakon ‘yan Isra’ila guda 11 da suke tsare da su, cikinsu har da wasu tagwaye ‘yan shekaru uku a daren jiya, wanda zuwa yanzu ya kawo adadin mutanen da aka saki sun kai 50

Haka zalika an kara  sako  Falasdinawa 33 daga gidajen yarin Isra'ila  wanda  suka  hada da yara 30 da mata uku.

Sa'o'i kadan kafin tsagaitawar bude  wuta  ta kwanaki hudu ta kare, Kasar  Qatar dake aikin shiga tsakani ta ce Isra'ila da Hamas sun amince da tsawaita wa'adin nan da  kwanaki biyu.

Kakakin Ma’aikatar  tsaron Amurka John Kirby ya ce a cikin kwanaki biyu masu zuwa, Hamas ta kuduri aniyar sake sakin wasu mata da kananan yara 20.

A ranar Litinin din da ta gabata ce wasu motocin dakon kaya dauke da kayan agaji suka shiga zirin Gaza tare da raba abinci da man fetur da magunguna da kungiyoyin agaji ke rabawa.