On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Sako Ragowar Fasinjojin Jirgin Kasa Da 'Yan Ta'adda Suka Sace A jihar Kaduna

JIRGIN KASA NA KADUNA

Rahotanni na baiyana cewa Yan ta’adda sun sako ragowar fasinjojin jirgin kasar da suka sace a ranar 28 ga watan Maris din bana.

Farfesa Yusuf  Usman ne ya tabbatar da hakan a madadin gwamnatin taraiyya  ta cikin wata sanarwa da ya fitar , inda ya baiyana cewa an sako mutanen ne da kimanin karfe  4 na yammaci.

Idan ba’a manta ba, yan ta’addar  da suka kaiwa  jirgin hari a kaduna  sun  rika sakin fasinjojin rukuni zuwa rukuni , wanda kuma kason karshe da suka saki  sune na ranar  19 ga waan Augustan Bana.

Kazalika an kama wanda  ke shiga tsakani mai suna Tukur  Mamu a ranar 6 ga  watan jiya a birnin Alkahira na kasar Masar a kan hanyarsa a zuwa Saudiya, inda aka damkashi hannun  Hukumar tsaro ta DSS, wanda ta zarga da tallafawa  yan  ta’adda.