On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Samu Alhazai Mata 75 'Yan Najeriya Dauke Da Juna Biyu A Saudiyya

Hukumar aikin hajji ta kasa ta ce kimanin Alhazai mata masu daukar da juna biyu 75 ne aka kwantar a wasu Asibitoci dake birnin Makkah da kuma Madina domin samun kulawar gaggawa.

Shugaban tawagar likitoci  na hukumar aikin hajji ta kasa,  Usman Galadima ne ya baiyana haka, Ya ce duk da fadakarwar da suka rika  yi  akan kauracewa  zuwa  aikin hajji  ga mata masu dauke da juna biyu, amma an samu wasu  da suka yi wa  fadakarwar  kunnen kashi.

Ya kuma baiyana cewar  tawagar  likitocin  na fama da larurori  da  maniyyatan  suka  fi fama dasu  kamar  ciwon siga da  hawan jini.

Kazalika  ya baiyana cewar  asibitin sha ka tafi  na hukumar  aikin hajji  ta kasa dake saudiyya  na samun karuwar  alhazan da ke  fama da rashin  lafiya.