On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Samu 'Karuwar Masu Amfani Da Internet Da Kimanin Milyan 7 A Najeriya

BRADBAND

Najeriya ta samu wani gagarumin cigaba ta bangaren amfani da hanyoyin sadarwa a cikin watanni bakwai da suka gabata daga watan Nuwamba 2021, inda aka samu sabbin mutane har miliyan bakwai da suka fara yin amfani da internet, wanda hakan ke nuna ci gaban da aka samu ya cimma kashi 70 cikin 100 da ake son cimmawa nan da shekarar 2025.

Shugaban  Hukumar Sadarwa ta Najeriya Farfesa Umar Danbatta, wanda ya  baiyana  alkaluman a cikin wata sanarwa, ya ce ci gaban da ake samu a hanyoyin sadarwa na internet  yana matukar tasiri ga sauran bangarorin tattalin arziki kamar kiwon lafiya, ilimi da noma  sai harkokin  kudi da sufuri da kasuwanci da  mulki da kuma sauran  wasu sassa.

A yanzu haka dai  Masu amfani da Intanet sun karu daga miliyan 90 a shekarar 2015 zuwa miliyan 150 da dubu  36 kamar yadda  kididiga ta nuna a  watan Mayun 2022.

Daga karshe, Ya  yabawa al’ummar kasar nan, bisa ga irin cikakken goyon bayan da  suke  bawa hukumar  a kowance lokaci  wanda haka yasa take samun nasarori masu yawan gaske, Sannan kuma yace hukumar zata  cigaba da  bijiro da sabbin tsare-tsare  da  zasu inganta   bangaren.