On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An samu Raguwar Masu Aikata Lefuka Da Babur Din Adaidaita Sahu A Kano

Shugaban Hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan’agundi, Yace dokar takaita zirga-zirgar Babura masu kafa ukku daga karfe 10 na dare zuwa washewar gari, ta haifar da ‘Da mai Ido.

Yace an samu gagarumar raguwar aikata lefuka a jihar nan, Sannan kuma babu wani lefi da aka samu an aikata  ta hanyar amfani da Adaidaita Sahu tun daga lokacin da dokar fara aiki.

ya kara da cewa hukumar zata cigaba da yin aiki domin tabbatar da bin doka da oda