On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

An Samu Sabbin Mutane Da Suka Kamu Da Corona A Najeriya - NCDC

Cibiyar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC ta tabbatar da karin wasu mutane 42 da suka kamu da cutar COVID-19 a cikin kasarnan cikin makonni biyu, inda jihar Legas ta samu karin mutane 27.

Hukumar NCDC ta bayyana haka ta cikin wani sako da aka wallafa a shafinta a karshen mako, inda ta kara da cewa an samu adadin mutanen a jahohin  Edo da Kano da Nasarawa da Kaduna da Plateau da kuma  Babban Birnin Tarayya Abuja.

Hukumar  tace sabbin alkaluman sun kawo adadin wadanda suka kamu da cutar ta Corona  a kasarnan zuwa dubu dari 2 da 66 da 492.

An samu sabbin mutanen ne tsakanin 31 ga Disamba na shekarar 2022 zuwa 13 ga watan Janairu da muke ciki na 2023.

A cewar rahoton, NCDC ta tabbatar da cewa Najeriya  ta samu sabbin mutane 29 daga ranar 7 zuwa 13 ga watan Janairu.

Sabbin mutanen sun fito ne daga Legas da aka samu 15 sai 5 a Abuja da 4 a Kano da 3 a Nasarawa da 1 a Nasara sai 1 a Plateau.

Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta kasa na ci gaba da bayar da shawara ga ‘yan Najeriya su karbi rigakafin COVID-19.