On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Samu Shugabanni Biyu a Hukumar Raya Yankunan Kan Iyaka ta Kasa

An fara fuskantar rikicin shugabanci a Hukumar Raya Yankunan Kan Iyaka ta Kasa (Border Communities Development Agency – BCDA), bayan Dakta Dakorinama Alabo George ya cigaba da zama a matsayin Babban Sakataren Zartarwa na hukumar duk da sanarwar da Fadar Shugaban Kasa ta yi na maye gurbinsa da tsohon dan Majalisar Wakilai, Abdulrazak Sa'ad Namdas.

Rahotanni sun bayyana cewa, George, wanda ke neman tikitin takarar gwamnan Jihar Rivers a karkashin jam'iyyar APC, ya ajiye mukaminsa domin shiga zaben fidda gwani, inda ya fafata da 'yan takara da suka hada da Gwamna Siminalayi Fubara da Kingsley Chinda da kuma Tonye Cole.

A ranar 26 ga watan Yuni, Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya sanar da nadin Abdulrazak Sa'ad Namdas a matsayin sabon Babban Sakataren Zartarwa na BCDA, a wani bangare na sabbin nade-naden da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da su.

Sai dai duk da wannan sanarwa, George na cigaba da gudanar da ayyukansa a hedikwatar hukumar da ke Abuja. Rahotanni sun ce yana zuwa ofis kamar yadda ya saba, kuma har yanzu yana jagorantar wasu harkokin gudanarwa na hukumar.

Majiyoyi daga cikin hukumar sun bayyana cewa har yanzu Namdas bai karbi ragamar shugabanci ba, lamarin da ya haifar da rashin tabbas kan wanda ke da ikon tafiyar da hukumar.

Wasu ma'aikata sun ce suna jiran karin umarni daga Fadar Shugaban Kasa kafin a gudanar da mika mulki a hukumance.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce kan yadda ake aiwatar da umarnin shugaban kasa dangane da nade-naden shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya, yayin da har yanzu ba a bayyana lokacin da za a kammala mika ragamar shugabancin hukumar ga sabon shugaban da aka nada ba.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thunder storm

    High: 33°C | Low: 23°C