On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Sauke Mukaddashin Babban Akanta Na Kasa Chukwuyere N. Anamekwe

AKAWU

Gwamnatin Taraiyya ta cire mukaddashin babban akantan kasar nan Mr. Chukwuyere N. Anamekwe inda aka maye gurbinsa da Mr. Okolieaboh Ezeoke Sylvis, wanda tsohon darekta ne a tsarin asusun gwamnati na bai-daya, TSA.

Wasu  Rahotanni sun baiyana cewa an maye gurbin mai rikon mukamin na Akanta-Janar din ne saboda hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa, EFCC, na bincikensa, yayin da wasu rahotannin kuma ke baiyana cewa an cire shi ne a sakamakon wasu kalamai  da  yayi a kwanan nan, inda ya baiyana cewa Gwamnati sai ta ciwo bashi take biyan albashin Ma'aikata

Anamekwe wanda aka nada shi a  matsayi na rikon-kwarya a ranar 22 ga watan Mayu bayan da hukumar EFCC ta kama tsohon Babban Akantan kasar nan, Ahmed Idris bisa zargin almundahana da naira biliyan 80, ya yi kalaman cin bashin ne.

Mista. Sylva, wanda ke zaman mukaddashin Babban Akantan a yanzu, rahotanni na nuni da cewa zai yi ritaya a cikin watanni uku na farkon shekara mai zuwa, 2023.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta kaddamar da neman wanda za ta nada a matsayin sabon Babban Akantan, kamar yadda bayanai ke nunawa.

Jaridar The Nation ta  ta ruwaito cewa duk wani kokari da ta yi na neman gaskiyar kalaman da Anamekwe ya yi cewa gwamnati na ciyo bashi ta biya albashi, ya ci tura.