On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An Sauke Wasu Jagororin Majalisar Dokokin Jihar Kogi

A yaune Majalisar Dokokin jihar Kogi ta sauke wasu Shugabanninta 4 tare da Dakatar da wasu 3 bisa samunsu da aikata lefin rashin Da’a.

Yan Majalisar sun dauki wanan mataki ne a yayin wani zaman gaggawa da suka yi a harabar  zauren maajlsiar, biyo bayan wani kudurin gaggawa da  Dan Majalisa Enema Paul na jam’iyyar APC ya gabatar.

Shugabannin Majalisar  da  aka dauki matakin saukewar a kansu, sun hada da  Ahmed Mohammed wanda ya  kasance Mataimakin kakakin Majalisar da bello Hassan Abdullahi shugaban Masu Rinjaye sai Ndako Idris  Mataimakin Shugaban Masu rinjaye da kuma Mister Edoko Ododo  mataimakin Bulaliyar Majalisar.

Kazalika daga bisani yan Majalisa 17 da suka dauki matakin, sun maye gurbin wadanda suka sauke da  Rabiu Alfa a matsayin Mataimakin Kakaki sai Bajeh Muktar  Shugaban Masu Rinjaye da umar Isa Mataimakin Shugaban Masu rinjaye da  kuma Enema Paul mataimakin Bulaliyar  Majalisar.