On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Sauyawa Shari'ar Zaben Gwamnan Jihar Kogi Matsuguni Zuwa Abuja

Shugabar Kotun Daukaka Kara, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta bayar da umarnin mayar da kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Kogi daga Lokoja zuwa Abuja.

A cewar wata sanarwa da David Umar Mike, sakataren kotun ya fitar, yanzu haka za a gudanar da dukkan shari’ar a cibiyar shari’a ta kasa da ke kan titin Umar ‘Yar’adua a birnin tarayya Abuja.

An bukaci masu kara da su lura  da sauyin da aka samu.

Yayin da sanarwar ba ta fayyace dalilin daukar matakin ba, wata majiya mai tushe a cikin kotun ta bayyana cewa an dauki matakin ne saboda fargabar matsalolin tsaro.

Majiyar ta bayyana cewa an sha kai hare-hare da dama ga ma’aikatan kotun a Lokoja, al’amarin da ya kai matsayin da rayuwarsu ke cikin hadari.