On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Shiga Makoki A Kwalejin Ilimi Ta Bichi A Kano

Kwalejin Ilimi ta tarayya dake Bichi a Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar Japheth Solomon, dalibin aji 2 na sashen koyar da Ilimin kasuwanci.

Cikin wata sanarwa da Fatima Hassan Ahmad Daraktar yada labarai da hulda da Jama'a ta kwalejin ta fitar, ta ce da yammacin ranar  Litinin 17 ga Yuli, 2023 kwalejin ta samu labarin wata takaddama da ta barke tsakanin wani dalibi a wajen makarantar mai suna Japheth Solomon da wani  dan kauyen Buden waje dake makwaftaka da makarantar.

Rahotanni sunce an yanku Japheth  a wuyan hannunsa inda bokan karatunsa ne suka garzaya da shi Babban Asibitin Bichi sai dai  ya zubar da jini da yawa kuma cikin duba lafiyarsa rai ya yi halinsa.

Fatima Hassan ta ce hukumar gudanarwar kwalejin ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a safiyar ranar talata 18 ga watan Yuli, 2023, inda ta gabatar da jawabi ga daukacin daliban Kwalejin tare da ayyana makokin kwana biyu.

Shugaban kwalejin Dr Bashir Sabo Abubakar ya yi kira ga daukacin daliban da su yi taka tsantsan wajen kare lafiyarsu. 

Kwalejin tace tana  aiki tare da 'yan sanda da sauran wadanda abun  ya shafa don tabbatar da  adalci akan al'amarin.