On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

An Ta Shi Ba Tare Da Cimma Matsaya Ba Tsakanin Gwamnati Da Nlc Kan Cire Tallafin Mai

An tashi batare da cimma wata matsaya ba a ganawar da aka yi tsakanin Gamaiyyar kungiyoyin kwadago na kasar nan, da kuma wakilan gwamnatin taraiyya kan batun cire tallafin mai, a daren jiya.

Ganawar dai  ta biyo bayan sanarwar da shugaban  kasa Bola  Tinubu  ya  yi  ta  cewar an kawo karshen  maganar  biyan tallafin mai a  kasar  nan, da  kuma sabon farashin litar man fetir  da  kanfanin mai  na kasa  ya  sanar  a jiya.

Da  yake  jawabi jim kadan bayan  tashi  daga  ganawar, Shugaban kungiyar kwadago  ta kasa, Kwamared Joe Ajaero,   ya  ce   za’a  cigaba da  tattaunawar,  kasancewar babu  wata  masalaha  da aka cimmawa  a yayin zaman nasu da wakilan gwamnatin taraiyya.

Kazalika  ya koka  kan yadda  kanfanin mai  na  kasa  ya sake kara  farashin man fetir kafin ganawar  da suka yi a  daren jiya.

Shima  da yake  nasa jawabin a madadin gwamnatin taraiyya, Daraktan  yakin neman zaben Tinubu da Shettima, Dele Alake,  Ya  ce  za’a  cigaba da tattaunawa  a tsakaninsu  domin samo  mafita  akan  matsalolin.