On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

An Tsayar Da Ranar Fara Kidayar Jama'a Da Kidayar Jama'a Da Gidaje A Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce za a fara aikin kidayar  jama’a da gidaje na 2023 a ranar 3 ga watan  Mayu dake tafe.

Wani mamba a kwamitin yada labarai da bayar da shawarwari kan kidayar yawan jama'a da gidaje na kasa na shekarar 2023, Dr Garba Abari, ya tabbatar da haka ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce aikin  na kwanaki uku zai fara ne daga ranar 3 ga watan Mayu sannan kuma za a kare a ranar 5 ga watan Mayu a fadin kasarnan.

Abari, wanda shi ne Darakta-Janar na Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa NOA, ya bayyana cewa, aikin kidayar zai kirga kowanne mutum da  gida a lungu da sako.