On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Tsinci Wani Yaro Da Ya Bace A Nan Kano A Kasar Togo

An samu wani Yaro Dan shekara 14 a duniya da ke unguwar Hotoro dake nan jihar Kano, wanda iyayensa suka sanar da bacewarsa a cikin watan Maris din bana, a kasar Togo.

Rahotanni sun baiyana  cewar  anga yaron  tare  da wani karamin yaro  wanda  shima ya fito daga Najeriya,Suna yin bara akan Titi a can kasar ta Togo,inda suke neman Abinci.

Majiyar  ta baiyana cewar an samu yaran  wajen wata ‘yar  Najeriya  da ta yi shuhura  wajen siyar da Abinci a kasar Togo  mai suna  Hajiya  Maijidda Mai Abinci, wanda  wasu mutane suka kai mata yaran, Kasance  sunce su  ‘Yan Najeriya ne.

Matar  ta baiyanar  cewar  a halin yanzu ita take  kula dasu,  a  yayin da tasa  ake neman iyayensu a nan Najeriya.

Hajiya mai  Abinci, ta baiyana cewar yaran sun fada mata  cewar  wata mata  ce  ta yi awon gaba dasu  daga nan Najeriya zuwa kasar Ghana, inda  suka yi ta rokonta  data  temaka  ta sake su,  Kafin daga  bisani  su tsinci  kansu a  kasar ta Togo.

Mahaifin yaron , Ya godewa  hajiya  mai Abinci  saboda kishin data nuna,  Tare da rokon Al’umma su temaka  masa,Kasancewar bashi da kudin da zai biya  domin dawo  da yaron nasa  gida  Hotoro dake nan Kano.