On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Yabawa Majalisar Wakilai Saboda Amincewa Da Kudirin Kafa Rundunar Peace Corps

Peace corps

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta kasa, Peace corps reshen jihar Kano, ta yabawa majalisar wakilai ta kasa bisa amincewa da kudirin dokar kafa rundunar, wanda a yanzu haka yake gaban majalisar dattawa domin samun amincewarta kafin tura shi wajen shugaban kasa don saka ma dokar hannu.

Babban kwamandan rundunar reshen jihar kano, Musbahu Ado Ibrahim CGPM ne ya yi wannan yabo,  ya ce matakin da majalisar wakilan ta dauka  abun a yaba mata ne, la’akari da irin yadda aka jima ana kishirwar ganin kafuwar rundunar  ta tabbata.

Musbahu Ado Ibrahim CGPM y ace makasudin kafa rundunar  shi ne domin wanzar da lafiya a tsakanin yan kasa tare da dafawa sauran hukumomin tsaro wajen kare  rayuka da dukiyoyin al’umma.

Daga nan sai ya yi kira  ga ‘yan kasa  das u rika temakawa hukumomin tsaro da bayanan kan duk wani bakon abu da basu amince da shi ba.