On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An Yiwa Mataimakin Shugaban Kasa Tiyata A 'Kafa

Hoton Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon fatan samun lafiya cikin gaggawa ga mataimakinsa, farfesa Yemi Osinbajo.

Sakon shugaban kasar na kunshe cikin wani sakon twitter da  Babban hadimin sa ta fuskar yada labarai da wayar da kai, femi Adesina ya wallafa.

Adesina yace shugaban kasar ya aike da sakon fatan murmurewa cikin gaggawa ga yemi Osinbajo, a sakamakon tiyatar da aka yi masa a ‘kafa a daren jiya.

A wani bangaren kuma, Yan Najeriya  sun yabawa Mataimakin Shugaban Kasa game da matakin da  ya dauka na yin amfani da Asibitin Gida tare kuma da baiyana halin da lafiyarsa ke ciki.

A daren jiya ne, Hadiminsa  ta  bangaren Yada Labarai, Laolu Akande ya wallafa wani sako a shafinsa na twitter, wanda ke tabbatar da cewa anyiwa mataimakin shugaban kasar, tiyata a ‘kafa sakamakon raunin da  ya ji a lokacin da yake wasan  kwallon  Squash.

Kazalika daga bisani likitocin Asibitin Duchess  na kasar Jamus wanda ke Ikeja a birnin ikko, inda aka kwantar da mataimakin shugaban kasar sun tabbatar da samun nasarar kammala tiyatar cikin koshin lafiya.

Yan Najeriya cikinsu hadda masu  sukar gwamnati mai ci sun yiwa mataimakin shugaban kasar  fatan samun sauki cikin gaggawa, tare da yaba masa kan yadda  yayi imanin da tsarin kiwon lafiyar kasar nan.

 

 

 

More from Labarai