On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Muna Alfahari Da Nasarar Aisha Binani A Gaban Kotu - Ministar Matan Najeriya Tallen

Ministar harkokin mata, Pauline Tallen, ta yaba da hukuncin kotun daukaka kara da ta yi watsi da soke zaben fidda gwanin da ya samar da Aishatu Binani a matsayin ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa a jam’iyyar Apc.

Kotun daukaka kara da ke zamanta a yola a wani hukunci  na bai daya ta yi watsi da hukuncin da karamar kotun ta yanke kan Emmanuel Bwacha da Aishatu Binani a matsayin ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar Apc na jihohin Taraba da Adamawa.

Kotun ta bayar da umarnin a sake mika sunayensu ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta a matsayin 'yan takarar gwamna na jam'iyyar Apc na jihohin biyu.

Ministar ta bayyana hakan ne a taron tattaunawa na mako-mako da tawagar sadarwar fadar shugaban kasa ta shirya a Abuja.

Tellen, wacce ta bayyana karancin mata a harkokin siyasa da sauran mukamai na shugabanci a matsayin babban koma baya ga cigaban kasarnan, ta yi kira da a dauki matakin tabbatar da kashi 50 cikin 100 na mata, tana  mai cewa kashi 35 da aka saba shigarwa na mata  ba sa iya aiki yadda ya kamata..