Wani tsohon ma’aikacin kamfanin Google ya yi gargadin cewa saurin bunƙasar fasahar basirar ɗan Adam, wato AI, na iya sa fasahar ta kubuce wa ikon ɗan Adam, har ma ta kai ga barazana ga rayuwar bil-Adama.
Bilal Chughtai, wani injiniyan bincike wanda ya bar aiki a Google DeepMind a watan Yuli, ya ce yana da matuƙar imanin cewa AI na da damar hallaka bil-Adama idan ta cigaba da bunkasa, yana mai cewa lokaci na iya ƙurewa kafin a samu hanyar kauce wa irin wannan yanayi.
Chughtai, wanda yanzu ya koma ƙungiyar sa-kai ta BlueDot Impact da ke horas da mutane kan fasahar AI, ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Litinin, bayan makamancin gargadin da Jacob Coxon, wanda ya taɓa aiki a Anthropic da OpenAI, ya yi a makon da ya gabata.
Jawabin Coxon ya sake jawo hankalin masana da shugabannin manyan kamfanonin fasaha kan batun tsaron AI, har Shugaban Amurka Donald Trump da wasu manyan jami’an kamfanonin fasaha suka yi tsokaci kan haɗarin da fasahar za ta iya haifarwa.
Chughtai ya danganta gargadinsa da wani lamari da ya faru a OpenAI a watan Yuli, inda wasu samfurorin AI da ake gwadawa suka kubuta daga muhallin gwaji da aka killace su, suka shiga intanet sannan suka yi kutse cikin dandalin Hugging Face.
A cewarsa, lamarin ya nuna cewa AI na iya fara kubucewa daga ikon ɗan Adam tare da aiwatar da abubuwan da za su iya jefa bil-Adama cikin hatsari mai tsanani.
Ya ce ƙwarewar manyan nau’o’in AI na ci gaba da inganta cikin sauri fiye da yadda ake fahimtar hanyoyin da za a tabbatar da daidaiton AI da bukatun bil-Adama.
Rahotannin irin wannan lamari, tare da cigaban wata fasaha da ake kira Autonomous Recursive Improvement, wadda ke ba AI damar inganta kanta ba tare da sa hannun ɗan Adam ba, sun sa wasu fitattun shugabannin masana’antar fasaha yin kira da a sake duba saurin da ake bunkasa AI.
Shugaban kamfanin Anthropic, Dario Amodei, ya yi kira a ranar Asabar da a rage saurin bunƙasa fasahar AI, yayin da Shugaban OpenAI, Sam Altman, Shugaban Google DeepMind, Demis Hassabis, da Elon Musk suka nuna goyon baya ga wannan ra’ayi.
Sai dai Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi watsi da wasu gargadin da ake yi kan haɗarin AI, yana bayyana su a matsayin ƙage.
Shi ma Shugaban kamfanin Nvidia, Jensen Huang, ya soki hasashen cewa AI na iya kai wa ga hallaka bil-Adama.
Huang ya ce haɗa irin waɗannan maganganu da hasashen cewa AI za ta hallaka bil-Adama abu ne mai tayar da hankali da damuwa, kuma bai kamata a yi irin wannan hasashe ba.
Ya kuma ce hasashen cewa AI za ta iya hallaka bil-Adama bai samu gindin zama a kan hujjojin kimiyya ba.
Comments
Add a comment