On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Ana Neman Yiwa Godswil Ta Leko Ta Labe Kan Takarar Shugabancin Majalisar Dattawa

Wasu rahotanni na baiyana cewar takarar da tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ke yi na zama shugaban majalisar dattawa ta gamu da cikas, yayin da wata majiya ta baiyana cewar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya janye goyon bayan da yake yi masa.

Idan ba a manta ba jam’iyyar (APC) ta bayyana amincewarta  da Sanata Godswill Akpabio da wasu mutane uku a matsayin jagororin majalisar dokokin ta kasa.

Sai dai matakin  bai yi wa wasu ‘ya’yan jam’iyyar dadi ba, musamman masu neman kujerar shugabancin majalisar dattawa da ta wakilai, biyo bayan fushinsu  da suka nuna kan daukar matakin.

Rahotanni sun baiyana cewar  Sanatoci musamman ‘yan yankin Kudu maso Yammacin kasar  nan , zasu  yi wata ganawa a tsakaninsu gobe,  domin baiyana matsayar su kan matakin.