On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ana Saran Gabatar Da Sunayen Ministoci A Yau

TINUBU

Yauce rana ta karshe da doka ta sahalle shugaban kasa ya mika jerin sunayen mutanen da yake son nadawa kan matsayin ministoci ga majalisar dokoki ta kasa domin tantancewa, Yayin da majalisar ke tsammanin karanta sunayen a zamanta na yau

Yau ce  ranar karshe da kundin tsarin mulkin kasa  ya kaiyade  ga  shugaban kasa  ya mika sunayen ga zauren majalisar dattawa, a cikin kwanaki  sittin da hawa karagar mulki.

Hadimin shugaban kasa  ta bangaren yada labarai, Jackson Akpabio ya tabbatarwa da manema Labarai a daren jiya cewar, Yaune za’a baiyana cikakkun sunayen mutanen da ake son nadawa kan matsayin ministocin.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya  da su dena yada  jita-jita a maimakon haka su dan tsahirta  domin jin sunayen a hukumance.