On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Ana Tambayar NNPCL Kan Tiriliyan 7.13

Ana ci gaba da tambayoyi kan yadda Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya kashe naira tiriliyan 7.13 kan abin da ya bayyana a matsayin tsaron makamashi a shekarar 2024.

Adadin kuɗin na ƙunshe ne a cikin rahoton binciken kuɗaɗen kamfanin na shekarar 2024, wanda aka fitar a watan Nuwamban 2025.

Ko da yake kamfanin bai fayyace abin da aka kashe kuɗin a kai ba, wasu masana sun yi hasashen cewa wataƙila an yi amfani da su wajen biyan tallafin man fetur ko kuma kare bututun iskar gas.

Yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan lamarin, NNPCL ba ta fitar da wata sanarwa ba, domin Babban Jami'in Hulɗa da Jama'a na kamfanin, Andy Odeh, bai amsa kiran waya ko saƙon da aka aike masa ba.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 35°C | Low: 23°C