On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Ana Zargin Tsohon Ministan Lantarki Da Sace Naira Bilyan 22

SALE MAMMAN

A yanzu haka tsohon ministan lantarki, Sale Mamman na a komar shalkwatar hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa dake Abuja, sakamakon zarginsa da almundahanar naira milyan dubu 22. An cafke tsohon ministan ne a ranar Laraba kamar yadda jaridar Daily trust ta baiyana.

Wata majiya ta fadawa  jaridar  cewar, Sale Mamman wanda  ya kasance  minister  shekarar  2019 zuwa 2021,ana  tuhumarsa da hada baki da  jami’an  ma’ikatar  lantarki, tare da karkatar da zunzurutun kudi  har  naira  milyan dubu 22  da aka  ware  domin  aikin samar  da tashoshin  lantarki na  Zungeru da  kuma  Mambila, inda  suka raba kudin a tsakaninsu.

Majiyar  ta kuma baiyana cewar  an gano  tarin kadarori  da dukiya  a  nan gida  Najeriya da kuma   kasashen waje  da ake alakanta su da  mallakin tsohon ministan ,  ya yi  da aka samu Milyoyin  naira da kuma Dalar  Amurika  a  hanunsa.

Rahotanni sun baiyana cewar  tsohon ministan lantarkin zai ci gaba da kasance a hannun hukumar  EFCC  har  zuwa  lokacin  da zata  samun bayanan da take bukata a wajensa.

Har  zuwa  yanzu dai  hukumar ta EFCC  bata  fitar da sanarwar  dakume  tsohon ministan lantarkin ba, kawo  yanzu da muke baku labarin.