On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Anci Tarar Gidan Talabijin Na Arise Milyan Biyu Sakamakon Batawa Tinubu Suna

TAMBARIN GIDAN TALABIJIN NA ARISE

Hukumar kula da kafafen yada Labarai ta kasa ta ci tarar gidan Talabijin na Arise Milyan Biyu, a sakamakon yada wani rahoton bogi kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

An zargi tashar Tabajidin din da fitar da wani rahoto, wanda ta baiyana cewa, Hukumar zabe ta kasa na binciken Tinubu kan zargin da ake masa da yin hada-hada ta miyagun kwayoyi.

Sanarwar da aka ce ta fito daga hukumar zabe ta kasa, ta bazu a shafukan sada zumunta, amma daga bisani hukumar zaben ta karyata wannan rahoto, wanda  ta baiyana a matsayin wani aikin masu yada labaran kanzon kurege.

A ranar Lahadin data gabata ce, Gidan Talabijin na Arise ya nemi Afuwar Tinubu kan fitar da rahoton na bogi.

More from Labarai