On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Anyi garkuwa da 'yan mata na kwalejin lafiya ta Zamfara

Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara  ta ce jami’an tsaro...

 

Wasu 'yan bindiga sunyi awon gaba da ɗalibai mata hudu a  kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Jihar Zamfara  a cikin  daren Ranar Talata.

Wani mazaunin yankin ya faɗa wa kafar yada Labarai ta  BBC cewa maharan sun afka wa gidan da ɗaliban ke zaune wanda ke wajen makarantar a garin Tsafe bayan sun tarar da jami'an tsaro na gadin kwalejin.

Shugagan kwalejin, Yusuf Idris Maradun, yace ɗalibai biyar 'yan bindigar suka kama amma daga baya suka saki ɗaya daga cikinsu saboda ta kasa tafiya sakamakon lalurar ƙafa.

Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara  ta ce jami’an tsaro sun duƙufa wajen ganin an ceto ɗaliban da aka sace a gidan da suka kama haya suna kwana a cikin garin na Tsafe.