On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Anyi Hada-Hadar Kudi Ta Sama Da Bilyan 80 A Bangaren eNaira.

BUHARI DA GWAMNAN BABBAN BANKIN KASA CBN

Gwamnan Babban bankin kasa, Godwin Emefiele , Ya ce yawan hada-hadar kudi da aka yi ta hanyar amfani da tsarin nan na eNaira ya kai naira milyan dubu 8 a kasar nan.

Da yake  jawabi a Abuja, Gwamna Emefiele , Yace  an samu dimbin nasarori tun bayan kaddamar da tsarin  da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar dashi a cikin watan Oktoban 2021.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin  mataimakiyarsa  mai kula da shashin  ingancin kudi, Aisha Ahmad, Ta  ce  tsarin na eNaira  yana haifar da Da mai ido.

Kazalika shima da yake nasa jawabin, Mataimakin Gwamnan babban bankin kasa kula da sashin tsare  tsaren tattalin arziki, Kingsly Obiora, Yace  ya zuwa  wannan lokaci, an sauke  manhajar yin hada-hadar  kudi ta eNaira har Dubu 927.