On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Anyi Zanga-zangar Adawa Da Dokar Zaman Gida Da IPOB Ta Saka A Enugu

ENUGU

Mazauna birnin Enugu sun yi zanga-zangar nuna adawarsu da dokar zaman gida a duk ranar Litinin da haramtacciyar kungiyar ‘Yan aware ta IPOB ta saka

Mazauna birnin dake karkashin gamaiyyar  kungiyoyin farar hula  sun yin zanga-zangar  lumana tare da yin kira  ga jama’a  da su rika fitowa wuraren kasuwancinsu  na  yau da  kullum.

Jagoran masu zanga-zangar, Onyinye Mammah, Ya  ce  sun shirya gangamin ne  sakamakon yadda  dokar  zaman gidan ke cigaba da  illata masu  kasuwancinsu da  kuma  tattalin arziki  na yankin kudu maso gabashin kasar nan.

A wani bangaren kuma,  Jami’an hukumar raya birane  ta jihar Enugu sun rika rufe shagunan mutanen da  suke kin bude shagunan  su saboda  yin biyayya  ga dokar  zaman gidan.