On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

APC Na Jiran Dawowar Tinubu Kafin Yanke Hukunci Kan Nada Shugabannin Majalisar Dokoki Ta Kasa

APC

shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, Ya amince da cewar ba a tuntubi masu neman mukamai daban-daban a majalisar wakilai ta kasa ba, kafin a cimma matsaya kan yin amfani da tsarin shiyya-shiyya wajen fitar da mukaman.

Adamu ya baiyana haka ne  a  sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da ke Abuja lokacin da wasu masu neman kujerar shugaban majalisar dattawa suka yiwa shalkwatar  jam’iyyar  tsinke  domin nuna  fushinsu.

Sanata Abdullahi Adamu ya ce  jam’iyyar  zata sake yin  karatun ta nutsu  kan tsarin domin yin abunda  ya dace.

Sai dai ya baiyana cewa jam’iyyar ba za ta iya yanke   wani  hukunci  kan lamarin ba, ba tare da tuntubar  zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba.