On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

APC Ta Bukaci Kwankwaso Ya Dawo Jam’iyyar Kafin Lokacin Ya Kure

Jam’iyyar APC ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kano kuma mai rike da tutar takarara shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ya koma jam’iyya mai mulki.

Da yake magana da manema labarai ranar Lahadi a Abuja, mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa, Yakubu Murtala Ajaka, ya bukaci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP da ya amsa gayyatar koma APC  tun kafin lokaci ya kure.

Ajaka ya kuma gargadi Kwankwaso da  cewa cin zabe a  jiha daya ko biyu bai wadatar ya dora shi akan karagara mulkin shugaban kasa ba, yana mai cewa tsohon gwamnan na Kano yana da kyakkyawar dama ta zama shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Ya kuma yi wani shagibe da zolaya ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi da kungiyarsa ta ‘Obidient’, wadda ya ce a shafukan sada zumunta ne kawai take wanzuwa. Ya ce lokacin da aka fara kada kuri’a ta hakika a babban zaben 2023; 'Yan Najeriya za su Fidda da Aya daga tsakuwa.