Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Edo ta ayyana 'yan takarar Jam'iyyar APC a matsayin waɗanda suka lashe dukkan kujeru 18 na shugabannin ƙananan hukumomi da kujeru 192 na kansiloli a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar ranar Asabar.
Shugaban hukumar, Jonathan Aifuobhokhan, ya ce an gudanar da zaɓen a dukkan ƙananan hukumomi 18 da kuma gundumomi 192 na jihar bisa tanade-tanaden dokar zaɓe.
Ya ce zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali duk da wasu ƙananan matsalolin gudanarwa da ba su shafi sakamakon zaɓen ba. Ya kuma bayyana cewa za a miƙa takardun shaidar cin zaɓe ga waɗanda suka yi nasara a ranar Litinin.
Hukumar ta buƙaci duk wanda bai gamsu da sakamakon zaɓen ba da ya bi hanyar doka domin neman hakkinsa, tare da yin kira ga waɗanda aka zaɓa da su gudanar da mulki cikin riƙon amana da adalci ga kowa.
Comments
Add a comment