On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Asibitin Koyarwa Na Malam Aminu Kano Zai Fara Dashen Bargo

HOTON ASIBITIN KOYARWA NA MALAM AMINU KANO

Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, Zai fara Dashen Bargo wanda hakan zai sa ya zama na biyu cikine jerin asibitocin koyarwa dake kasar nan, da suke yin irin wanan aikin.

Shugaban Asibitin Farfesa Abdulraham Abba Sheshe ne ya baiyana haka yayin kaddamar da sashin kula da cututtukan da suka shafi  jinni, wanda wani dan asalin jihar Kano, Injiniya  Umar Ibrahim ya samar.

Ta cikin wata sanarwa  da Daraktar Hulda da jama’a ta Asibitin Hauwa Mohammed  Abdullahi ta fitar, Ta baiyana cewa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas ne kadai ke yin Dashen Bargo a kasar nan.

KASHI 22

Hoton Bargo

Daga nan sai ya godewa  Injiniya Umar  sanan kuma yayi masa addu’ar samun tukwici da gidan Aljanna.