On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Asisat Oshola Ta Lashe Kyautar Gwarzuwar 'Yar Wasan Afrika Ta Bana

Yar Wasa Asisat Oshola

'Yar wasar gaba ta kungiyar kwallon kafaer Mata ta kasa Super Falcons Asisat Oshoala ta lashe kyautar gwarzuwar Yar wasa ta Afirka karo na biyar.

Oshoala, wadda ke buga  wasanta a kungiyar  kwallon kafa  ta  Barcelona, ​​  ta  doke Grace Chanda  daga kasar  Zambia da Ajara Nchout Njoya  daka kasar  Cameroon wadda  ke bugawa  kungiyar kwallon kafa ta  Inter Milan  wajen lashe  kyautar.

Nasarar data  samu, tasa  ta  zarce 'yar wasa Perpetual Nkwocha a matsayin 'yar wasan da ta fi  lashe  kyautar gwarzuwar yar wasa  ta nahiyar  Afirka.

Oshoala mai shekaru 27, It ace  Yar  Najeriya daya tilo da aka  zaba domin  shiga cikin  jerin sunayen karshe  da aka tantance  domin  samun wanda zai lashe  kyautar a shekarar  2022.