On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

ASUP Ta Gargadi Gwamnoni 8 Su Biya Hakokin Mambobinta Kafin Karewar Wa'adin Mulki

Kungiyar Malaman Makarantun Fasaha a Najeriya ASUP tayi kira ga gwamnonin jihohin Abia da Osun da  Plateau da Benue  da Edo da  Ondo da  Ogun da kuma Sokoto da su biya albashin mambobinta kafin su kammala wa’adinsu  a ranar 29 ga Mayu na 2023.

Da yake zantawa da manema labarai a karshen taron kungiyar a ranar Alhamis, Shugaban ASUP, Anderson Ezeibe ya zargi gwamnonin da rashin nuna dattako tare da jefa malaman cikin wani hali a jihohinsu.

Ezeibe ya kuma yi kira ga ma’aikatar ilimi da ta mutunta hukuncin da kotun ma’aikata  ta kasa ta yanke, ta hanyar sallamar  shugabannin makarantun gwamnatin tarayya na Ugep da Shendam da Mungonu da Wannnune, da kuma Ohodo daga matsayin shugabanni na kwalejojin.