On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

ASUU Zata Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Yiwuwar Janye Yajin Aiki

Kungiyar malaman jami’o’in ta kasa ASUU da ke yajin aiki za ta yi wata ganawa a ranar Lahadi, 28 ga watan Agusta, domin yanke shawara kan ko za a dakatar ko kuma za’a ci gaba da yajin aikin kungiyar.

Majiyoyi daga mambobin kungiyar sun shaida wa manema labarai a ranar Litinin cewa taron zai gudana ne a shalkwatar kungiyar ta kasa da ke Jami’ar Abuja.

A halin da ake ciki, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ce ba ta da masaniya kan shirin haramta kungiyar ASUU.

Kakakin ma'aikatar, Ben Goong ya kuma nunar da  cewa gazawar kungiyar ta janye yajin aikin da take yi duk da tsoma bakin gwamnati bai dace ba.