On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Atiku Abubakar Yayi Alkawarin Farfado Da Masana'antun Da Suka Durkushe

ATIKU ABUBAKAR

A nan kuma, Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar Ya yi alkawarin farfado da masana’antun da suka durkushe a jihar Kaduna, da kuma kawo karshen Yan fashin Daji a jihar.

Da yake jawabi  a yayin gangamin  yakin neman zabensa da aka yi a filin wasa na Ranchess Bees dake Kaduna a yau, Atiku  Abubakar Yayi Alkawarin magance matsalolin da suka addabi jihar kaduna idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Kazalika shima mataimakinsa  Ifenyi Okowo, Yace mutanen kudancin kasar nan sun shirya tsaf domin zabar jam’iyyar PDP da kuma Dan takarar su na shugaban kasa a zabe mai zuwa, la’akari da nasarar da jam’iyyarsu ta samu a zaben gwamnan jihar Osun.

Shima a nasa jawabin, Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, Yace duk da cewar an hanasu  yin gangamin yakin neman zaben a wajen da suka tsara tun da farko, jam’iyyar ta nuna cewa koda a kan titi suka gudanar da gangaminsu, zasu samu nasarar da ake bukata.

More from Labarai