On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Atiku Da Obi Zasu Garzaya Kotun Koli Domin Kalubalantar Nasarar Tinubu

‘Yan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour, Sunyi fatali da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke, na sake tabbatar da nasarar da Bola Tinubu ya samu a zaben da ya wuce.

A hirarsa da manema Labarai a daren jiya, jim kadan bayan kammala  zaman  kotun, Lauyan Atiku, Chiris Uche, Ya ce ya samu umarni daga  wajen wanda  yake karewa, kan cewar  zasu  daukaka kara  zuwa  kotun koli.

Haka zalika shima  mashawarcin jam’iyyar  Labour  ta bangaren shari’a,  Kehinde Edun, Ya kudiri  aniyar  kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotun koli.

Mister Edun ya baiyana bacin ransa da yadda  hukuncin kotun ya kasance, Inda  ya baiyana  cewar Kotun  bata yi masu adalci ba,  ta  yadda  ta yi watsi  da  shaidu guda  10 daga cikin 13 da  suka  gabatar mata, wanda  hakan ya yi babban lahani  ga  karar da suka shigar gaban kotun.