On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Atiku Ya Bukaci A Dakatar Da Gbajabiamila

Tsohon Mataimakin shugaban kasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya buƙaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da shugaban Ma'aikatansa, Femi Gbajabiamila, domin bai wa bincike mai zaman kansa damar gudana kan zarge-zargen cin hanci da ake yi masa.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar, Atiku ya ce bai kamata a yi watsi da waɗannan zarge-zarge ba.

Ya kuma yi nuni da yadda tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya dakatar da tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, yayin da ake gudanar da bincike kan zarge-zargen cin hanci da suka shafe shi.

Atiku ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da amfani da ma'auni biyu wajen yaƙi da cin hanci, yana mai cewa tana gurfanar da 'yan adawa idan ana zarginsu da rashawa, amma tana yin shiru idan zarge-zargen sun shafi manyan jami'an gwamnati.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 33°C | Low: 23°C