On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Atiku Ya Buƙaci Tinubu Ya Yi Murabus

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi afuwar 'yan Najeriya tare da yin murabus kan abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarin ɓoye gaskiya a takaddamar asusun Hukumar nan ta bogi.

Kiran na Atiku ya biyo bayan saɓanin bayanan da Babban Bankin Najeriya (CBN) da Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF) suka gabatar kan lamarin.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a yau.

Atiku ya ce bayanan da CBN ya gabatar a gaban Majalisar Wakilai sun yi karo da bayanan Ofishin Akanta Janar, lamarin da ya jefa gwamnatin Tinubu cikin wani babban rikicin amincewa da gaskiyarta.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 35°C | Low: 23°C