On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Atiku Ya Gana Da Dattawan Jam'iyyar PDP Na Majalisar Dattawa

ATIKU DA SHUGABAN JAM'IYYAR PDP

A ranar Talata ne Dattawan Jam’iyyar PDP dake zauren majalisar dattawa ta kasa suka gana da Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da kuma Mataimakinsa Gwamna Ifeanyi Okowa.

Taron wani bangare ne na kokarin sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar da suka harzuka  gabanin babban zaben kasar nan dake  tafe.

Wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka hada da gwamna Nyesom Wike  na daga cikin wadanda suka nuna rashin  jin dadinsu game da yadda harkokin jam’iyyar ke kasancewa.

To sai dai kuma  Atiku Abubakar Yaci alwashin sake hada kan yayan jam’iyyar wuri daya gabanin zabe mai zuwa. Daga cikin wadanda suka halarci ganawar hadda  shugaban jam’iyyar na kasa  Iyorchia Ayu.