On Air Now

ZANGON MARAICEN LAHADI

6:00pm - Midnight

Atiku Ya Kalubalanci Ƙarin Kuɗin Jarabawa

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki shirin sanya kuɗin naira 50,000 ga ɗaliban da za su rubuta jarabawar WAEC da NECO daga shekarar 2027.

A cikin wata sanarwa, Atiku ya kuma yi Allah wadai da ƙarin kuɗin makarantu na Kwalejojin Tarayya yana mai bayyana matakan biyu a matsayin marasa tausayi ga iyalan da ke fama da matsin tattalin arziki.

Ya yi gargaɗin cewa ƙarin kuɗin ilimi zai iya ƙara ta'azzara matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, tare da ƙara rage damar shiga manyan makarantu ga ɗalibai daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta janye shirin ƙarin kuɗaɗen, tare da ƙara zuba jari a harkar ilimin gwamnati da bunƙasa kayayyakin more rayuwa a makarantu.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 35°C | Low: 23°C