On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Atiku Ya Lashi Takobin Yin Aiki Tare Da Matasa Idan Har Aka Zabe Shi A Matsayin Shugaban Kasa

ATIKU ABUBAKAR

Dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, Ya sake nanata kudirinsa na tabbatar da an samu cigaba ta bangaren shigar da matasa cikin harkokin siyasa da kuma jagoranci.

Bayanin hakan ya fito ne  ta bakin Hadiminsa na musamman ta bangaren yada Labarai, Abdurasheed Uba Sharada, a yayin wata hira ta musamman  da aka yi dashi ta wayar salula, Inda ya  bada  tabbacin  kaso 40 bisa 100 na nade-naden da za’a yi a gwamnatinsa zasu tafi ne wajen matasa.

Kakakin Dan takarar shugaban kasar mai shekara 33 a duniya, wanda a kwanan nan ne aka yi masa nadin, Ya  fadawa wakilinmu Abdurrahman Balarabe Isah cewa, Maigidan nasa  ya himmatu  wajen ganin matasa masu kishi da fikira sun kasance  jagororin kasar nan a nan gaba kadan.

Bugu da kari ya baiyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar  a kowane lokaci  yana yin tafiya ne tare da jajirtattun matasa yan kasa ta bangaren kasuwanci da kuma Siyasa.