On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Atiku ya Soki Gwamnatin Tinubu akan Yadda Take Kashe Kudaden Kasa

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sama da naira biliyan 210 da aka cusa sau biyu a kasafin kudin 2026 ya nuna gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na cikin gwamnatocin da suka fi yin wakaci ka tashi da dukiyar kasar nan.

A cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa kan Harkokin Sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce wannan rahoto hadi da yadda Najeriya ta samu koma baya da kusan kaso 90 cikin 100 na ma'aunin cigaba da walwala na duniya sun fallasa cewa matsalar kasar ba rashin albarkatu ba ne, illa gazawar shugabanci.

Ya ce gwamnati ta bukaci 'yan Najeriya su sadaukar da kai ta hanyar cire tallafin mai, hada farashin musayar kudade da karin haraji, amma ta kasa bayyana yadda aka samu maimaita tanadin fiye da naira biliyan 210 a kasafin kudi.

Atiku ya kuma ce ikirarin cewa an cire tallafin man fetur, yaudara ce kawai ga 'yan Najeriya, yana mai nuni da rahoton kudi na NNPCL na shekarar 2024 wanda ya nuna an kashe naira tiriliyan 7.13 a karkashin abin da kamfanin ya kira "Energy Security Expenses", wanda ya ce a zahiri tallafin fetur ne.

A cewarsa, hakan na nuna cewa ba a taba cire tallafin gaba daya ba, sai dai an sauya masa suna tare da cigaba da daukar nauyinsa daga asusun gwamnati.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya ce rashin da'a wajen tsara kasafin kudi na lalata amincewar jama'a da masu zuba jari ga gwamnati, yana mai cewa yayin da jami'an gwamnati ke yabon wasu alkaluman tattalin arziki, 'yan Najeriya na fama da yunwa, tsadar rayuwa, rashin aikin yi, rufe kananan sana'o'i da matsalolin tsaro da ke hana manoma noma.

Ya kara da cewa duk wata gyara ta hakika dole ne ta fara da gwamnati ta nuna gaskiya da da'a iri daya da take bukata daga al'umma.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 33°C | Low: 23°C