Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar (ADC), Atiku Abubakar, ya soki kalaman Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa rayuwar al’ummar Najeriya na ci gaba da inganta.
A cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Phrank Shaibu, ya sanya wa hannu, Atiku ya ce kalaman shugaban ƙasar sun nuna akwai babban gibi tsakanin masu mulki da al’ummar da suka zaɓe su.
Ya ce duk da cewa Shugaba Tinubu ya gaji ƙalubale daga gwamnatocin baya, amma ba a zaɓi shugaban ƙasa domin ya riƙa ba da uzuri ba.
Atiku ya ƙara da cewa bayan fiye da shekaru uku a kan mulki, gwamnatin Tinubu ba za ta ci gaba da ɗora alhakin matsalolin ƙasa kan gwamnatocin da suka gabace ta ba.
Comments
Add a comment