On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Attajirin Amurika Ellon Musk Ya Soke Shirinsa Na Siyen Kanfanin Twitter

Ellon Musk

Attajirin Amurika Elon Musk, Yace Ya soke yarjejeniyar Siyar kanfanin Twitter akan kudi Dala Bilyan 44, Inda ba’a manta ba Dan Kasuwar ya kulla cinikayyar shafin ne a cikin watan Afrilun Bana.

Wata wasika dauke dasa hannun Lauyansa, Mike Ringler, Yayi ikirarin cewa, Kanfanin na twitter bai cika sharuddan da aka wajabta masa ba, inda ya kasa bayar da  cikakkun bayanai akan harkokin kasuwancinsa kamar yadda aka bukata.

Yace  kanfanin na twitter shine ya gaza cika ka’idojin da aka shimfida na yin cinikin.

Har zai  dai babu wani martani da aka samu daga kanfanin na Twitter.