On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Audu Mai Kaba Ya Zama Sabon Mai Horas Da Kano Pillars

MAI KABA

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da Abdu Maikaba a matsayin sabon mai horas da tawagar sai masu gida ta kano Pillars,inda ta kulla kwantiragin shekaru biyu da shi.

Audu Maikaba zai samu temakon  Abubakar Abubakar wanda aka fi sani da Senior  sai Ahmed  Garba Yaro-ro da  Gambo  Muhammad  da kuma  Auwalu  Abbas  a matsayin mai horas da mai  tsaron  raga  na  kungiyar.

A yayin kwarya-kwaryar  bukin kaddamar da sabon mai horaswar, Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdul Salam  ya bukace  da  ya zage damtse wajen  ganin ya  farfado da martabar  kungiyar.

Ya kuma baiyana cewar  gwamnatin kano a shirye  take  ta  bada duk wani goyon bayanta  wajen cigaban kungiyar , tare da bada  tabbacin cewar nan bada jimawa ba  gwamnati zata  gyara  filin wasa na  Sani Abacha dake  Kofar mata.

Shima  shugaban kungiyar, Alhaji  Babangida Umar Litle yace  nadin da aka yiwa  Abdullahi Maikaba  anyi shine bisa cancanta kuma  suna da kwarin gwiwar cewar  zai farfado  da kungiyar.