On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Ba Wani Tallafin Inganta Aiki da Kannywood ke Samu Daga Gwamnati - Maishadda

Kwararren mai shirya fina-finai a masana’antar Kannywood, Abubakar Maishadda ya koka kan karancin tallafi da masana’antar ke samu daga gwamnati da kuma sauran masu hannu da shuni a jihar, duk da tulin aiyukan yi da take samarwa.


Mai Shadda ya yi wannan kira ne jim kadan bayan kammala shirin “Mu Leka Kannywood” na nan Arewa Radio a jiya asabar.
Ya ce masana’antar na bukatar tallafi wajen karo ilimi da samun kwarewa a fannoni daban-daban na shirya fina-finai da kuma kayan aiki na zamani domin yin gogayya da takwarorin su na kudi.

Ya kara da cewa dukkan cigaban da aka samu a masana’antar tsahon shekaru da dama, an same su ne bisa kokarin yayan ta ba tare da wani tallafi daga gwamnati ba, duk da cewa a yanzu an fara samun kamfanoni masu zaman kan su na daukar nauyin wasu daga cikin shirye-shiryen su.

“Zaman kan mu muke a wannan masana’antar tsahon lokaci da yawa, ba wani tallafi da muke samu don ko bangaren kamfanoni masu zaman kan su, duk da cewa an fara samu, ba kowanne ne yake iya daukar nauyin fina-finan mu ba”.

“Amma ina tabbatar muku da cewa idan aka ba mu tallafin da muke bukata, za mu inganta aikin, kamfanoni za su kara gamsuwa da ingancin abunda muke yi kuma za su sa kudin su sosai domin samar da karin aiyukan yi da wannan babbar masana’anta ke samarwa.”

Mai shadda ya kara da cewa babban burin sa shine Kannywood ta fara samar da fina-finai da taurari da za su yi lokaci a ciki da wajen Najeriya tare da kulla yarjejeniyar aiki da manyan kamfanoni na kasa-da-kasa.

Ya ce yana da yakinin cewa nan gaba kadan masana’antar za ta fara shirya gawurtattun fina-finai da za’a haska a Netflix, Prime Video da sauran manhajojin kallon fina-finai na duniya.

“Yanzu ka kalli Prince Daniel Aboki, makon da ya gabata na kalli guda daga cikin fina-finan sa mai suna Kaka a manhajar Prime Video, wanda ya bayu saboda irin kokarin da yake, wajen shirya fina-finan sa.”

Yace irin tasirin da fina-finan Hausa da aka shirya a Kannywood za su iya yi kenan idan yan masana’antar suka samu horo da kayan aikin da ya kamata, yana mai karawa da cewa hakan zai samar karin kudin shiga ga gwamnati ita kan ta.

Da yake magana dangane da yadda siyasa ta raba kan yan Kannywood, Maishadda ya ce ya daina shiga harkokin siyasa saboda wasu abubuwa da suka fara da yake da na sani akan su, saboda wasu abubuwa da suka faru.

A cewar sa duk da ya samu kudi lokacin da ya yi siyasa, amma ya gane cewa ba za ta taba basi kudin da harkar fim ke ba shi ba.
 

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 33°C | Low: 23°C