On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ba Wata Yarjejeniya ta Biyan Wani Kaso na Alawus din Masu Rejistar Haihuwa - ALGON

Ƙungiyar Ƙananan Hukumomin Najeriya reshen jihar Kano, ALGON, ta ce ba ta kulla wata yarjejeniya ta biyan kasho 25 cikin 100 na alawus ɗin masu rajistar haihuwa na unguwanni da masu kula da shirin a ƙananan hukumomi, a ƙarƙashin shirin rajistar haihuwa ba.

Mai magana da yawun ALGON, Surajo Ibrahim Imam, ya bayyana hakan ne a wata hira da Arewa Radio bayan wasu masu rajistar haihuwa sun yi iƙirarin cewa masu daukar nauyin shirin sun amince za su biya kaso 75 cikin 100 na alawus ɗinsu, yayin da ALGON za ta biya sauran kaso 25.

Imam, wanda kuma shi ne shugaban ƙaramar hukumar Dala a Kano, ya ce ALGON za ta gudanar da wani taron gaggawa da ma’aikatan da abin ya shafa domin tattauna batun da kuma samo mafita.

A cewar sa, kungiyar ta sub a za ta yadda a tsaida shirin rejistar haihuwar ba saboda muhimmancin sa wajen tsara cigaban kasa.

Ya buƙaci masu rajistar haihuwa da masu kula da shirin a ƙananan hukumomi da su yi haƙuri, ganin yadda wasu daga cikinsu suka kwashe watanni ba tare da samun alawus ɗin da ya kamata a biya su ba.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 34°C | Low: 23°C