On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Ba Za'a Rubuta Jarabawar NECO A Ranar Babbar Sallah Ba, Inji NECO.

TAMBARIN HUKUMAR NECO

Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Makarantun Sakandire Ta Kasa, NECO, Ta baiyana cewa bata tsara cewar za’a rubuta jarabawa a ranar 9 ga watan da muke ciki ba, Sabanin wasu rahotanni dake baiyana cewa Hukumar ta saka jarabawa da za’a a yi a ranar Idin Babban Sallah.

Hukumar ta baiyana haka ne ta cikin wata sanarwa mai dauke dasa  hannun shugaban sashin yada labaranta da kuma Hulda da Jama’a, Abdul’aziz  Sani wadda aka rabawa manema labarai yau a Abuja.

Ya kara da cewa Hukumar  tana sane da irin muhimmancin bukukuwan da suka shafi addini suke dashi,  wanda  hakan yasa take yin tanadi na musamman wajen saka ranar da za’a gudanar da jarabawa a irin wannan lokaci.

Idan za’a iya tunawa an fara  jarabawar Kammala Manyan Makarantun Sakandire  ta kasa a ranar  27 ga watan jiya, Sannan kuma  za’a kammala ta a ranar  12 ga  watan  Augustan bana.