On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Babban Bankin Kasa Ya Ce Babu Lokacin Dena Yin Amfani Da Tsaffin Takardun kudi

KUDI

Babban bankin kasa CBN, Ya ce tsaffin takardun kudi na naira da aka sauyawa fasali zasu cigaba da yin aiki har sai abunda hali ya yi.

Idan  ba’a manta ba,  A cikin watan  Octoban  bara ne, Babban bankin kasar  ya  bullo da sabbin takardun kudi yan naira  200 da  500 da  kuma  naira  dubu 1, Sannan  kuma ya saka  wani  wa’adi  da za’a dena amfani da tsaffin  takardun kudin a wancan  lokaci.

To sai dai a sanarwar da Babban bankin kasar  ya fitar a  ranar Talata,  Ya ce  yana sanar da al’umma cewar  ya tsawaita  wa’adin cigaba da amfani da tsaffin takardun kudi  yan naira  200 da  500  da kuma  dubu  1 har  sai  abunda  hali  ya  yi.

Sanarwar wadda  ta fito ta hannun kakakin babban bankin Isa Abdulmumin,  Ya ce rassan babban bankin kasa  zasu  cigaba da  karbar  tsaffi da kuma sabbin takardun kudi  daga  hannun  bankunan  ajiya.

Haka zalika bankin ya  ce yana  aiki tare da hukumomin da abun ya shafa  domin ganin an janye hukuncin  da kotu  ta  yanke kan amfani da sabbin takardun kudin  nan  bada jimawa  ba.