On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Babban Bankin Kasa Ya Kara Kudin Ruwa

Mukaddashin Gwamnan Bankin Kasa

Babban bankin kasa CBN ya kara kudin ruwa daga kashi 18.5 zuwa kashi 18.75 cikin dari.

Mukaddashin gwamnan babban bankin kasa CBN, Folashodun Shonubi ne ya bayyana hakan a ranar  Talata  bayan taron kwamitin kula da harkokin kudi na bankin  a Abuja.

Wannan shi ne mataki na farko da kwamitin kudi ya yanke tun bayan hawan Shugaban kasa  Bola Tinubu kan karagar mulki a ranar 29 ga  watan  Mayun 2023.

Mukaddashin gwamnan babban bankin kasar  ya  ce  kara kudin  ruwan  ya taka rawar gani wajen samun  matsakaicin hauhawar  farashin  kayayyaki a kasar nan.